
Rahotanni na cewa, ana zargin an baiwa wasu ‘yan jam’iyyar APC mukami a hukumar zabe me zaman kanta, INEC dan su taimakawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yaci zabe.
Kungiyar fafutuka dake saka ido kan yanda akw gudanar da Gwamnati me suna SERAP ce ta yi wannan zargi inda tace tana neman shugaban kasar da ya duba wannan zargi da ake idan gaskiyane a cire wadannan mutane.
SERAP tace kamata yayi a maye wadannan mutane da ‘yan kasa na gari masu kishi wadanda basu da alaka da kowace jam’iyya.
Mataimakin Darakta na SERAP, Kolawole Oluwadare ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ranar 7 ga watan Yuni inda yace barin wadannan mutane a cikin INEC zai sa mutuncin da ake ganin hukumar dashi da gaskiya ya zube.
Wadanda ake zargin ‘yan APC dinne dake aiki a hukumar INEC sune kamar haka, Etekamba Umoren (Akwa Ibom), Isah Shaka Ehimeakne (Edo), Bunmi Omoseyindemi (Lagos), da Anugbum Onuoha (Rivers),