
Sakataren jam’iyyar APC, Ajibola Basiru ya bayyana goyon bayan jam’iyyar su ga matakin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.
A sanarwar da ya fitar daga kasar Saudiyya, Basiru yace lamuran tsaro sun runcabe a jihar Rivers amma gwamnan jihar ya ki tashi tsaye ya dauki mataki.
Yace suna fatan wannan mataki da shugaban kasa ya dauka ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya kara da kira ga shugaba Tinubu da ya dauki irin wannan mataki akan jihar Osun inda ya zargi gwamnan jihar da dakile ayyukan kananan hukumomi duk da umarnin kotu.