Wednesday, January 15
Shadow

APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso

APC ta Kano ta yi kira da a kama Kwankwaso

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta bukaci a kama jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma dan takarar Shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A wata Sanarwa da Abdullahi Abbas Shugaban APC a Kano ya fitar, jam’iyyar ta zargi Kwankwaso da yin zarge-zarge marasa tushe ga Gwamnatin Tarayya.

Dimokuradiyya TV ta ruwaito cewa, a yayin bikin kaddamar da aikin gina Titi mai tsawon kilomita 85 a garin Madobi, Kwankwaso ya ce Gwamnatin APC karkashin jagoranci Gwamnatin Tarayya na yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya a Kano.

Amma Abbas yace ba wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa Gwamnatin Tarayya.

Karanta Wannan  'Yan majalisar tarayya dake jam'iyyun Adawa sun nemi Gwamnati data biya ma'aikata Naira Dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Muna so mu yi kira ga jami’an tsaro da kakkausar murya da su kamo Kwankwaso, domin ya tona asirin wadanda ya kira makiyan Jihar Kano da ke yi wa Gwamnatin Tarayya aiki da masu tayar da kayar baya.” Inji sanarwar.

Shugaban ya kara da cewa, wadannan kalamai na nuni ne ga wata muguwar manufa da Kwankwaso da ‘yan tawagarsa suka yi na kawo tashin hankali a Kano.

Kwankwaso ya dade da zama barazana ga Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya bisa la’akari da al’amurran sa, inda ake zarginsa da daukar matasa wadanda mafi yawansu korarri ne daga makaranta domin tayar da tarzoma a Jihar.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu:EFCC ta kafa kwamiti dan binciken tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Abbas ya ce kafin zaben 2023 da kuma lokacin zaben 2023, an ɗauki dubban matasa tare da ba su damar tsoratar da jama’a wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, ta hanyar kai hare-hare da lalata kadarorin jama’a da kuma kwacen wayoyin hannu.

Shugaban ya yi zargin cewa a lokacin da aka dade ana takaddama a kan zaben Gwamnan Kano, Kwankwaso da mukarrabansa sun yi wa alkalai barazana.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *