
Rahotanni na tuna baya sun nuna cewa a lokacin tsohon kakakin majalisar Dattijai, Bukola Saraki, sun samu tirka-tirka da kakakin majalisa na yanzu, Sanata Godswill Akpabio kan maganar canja masa kujera.
A wancan lokacin, Sanata Godswill Akpabio ya nemi yayi magana da lasifikar dake kujerar sanata Ali Ndume amma Sanata Bukola Saraki ya hanashi inda yace ya koma kan wata kujera da ya canja masa wadda lasifikarta na aiki.
Saidai hakan ya jawo cece-kuce a majalisar inda a wancan lokacin aka zargi Bukola Saraki da aikata rashin Adalci.
A wannan karin ma, abinda ya jawo cece-kuce tsakanin Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti shine canja mata kujerar zama da kuma canja mata kwamiti.