
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar bashi da Alkawari.
Wike yace bai taba bibiyar Atiku ba.
Yace a shekarar 2019, Saraki, da Atiku da Secondus sun sameshi inda suka ce masa zasu bashi babban lauyan Gwamnati idan aka kafa Gwamnati.
Yace amma da aka fadi zabe bai san sanda aka kafa Kungiyar lauyoyin da zasu kai kara ba, yace shi da aka ce za’a baiwa babban lauyan Gwamnati ta yaya za’w masa haka.
Saidai yace dama hakan bai zo masa da mamaki ba dan yasan cewa Atiku dama bashi da Alkawari.
Dan haka Wike yace PDP bata shirya karbar mulki ba a kasarnan.
Yace shiyasa ya goyi bayan Tinubu kuma bai yi nadamar yin hakan ba.