Monday, December 16
Shadow

Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima

Atiku, Kwankwaso: Dalilan Da Ya Sa Arewa Ba Za ta Iya Magana Da Murya Ɗaya Ba A 2027 – Buba Galadima.

DAGA: Abbas Yakubu Yaura

Wani jigo a jam’iyyar, NNPP, Buba Galadima ya ce ba zai taba yiwuwa ɗaukacin yankin Arewa su samu ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya a zaɓen 2027 ba.

A wata hira da jaridar Sun, tsohon sakataren rusasshiyar jam’iyyar CPC, ya bayyana cewa a tsarin dimokuradiyya irin na Najeriya, masu zaɓe na da ƴancin yin zaɓi daban-daban.

Da aka tambaye shi ko ƴan Arewa za su zaɓi Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ko kuma takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Galadima ya ce, “Ba ma cikin còci; Ba ma cikin másallaci. Me ya sa za mu yi magana da murya ɗaya?

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan ci gaba da tattaunawa da Gwamnati

“Dimokradiyya kenan.”Idan ka haɗa mutane uku tare, kowa ya sami hanyar tunani daban-daban kan yadda za a magance wata matsala.”

Shugaban na NNPP ya kuma yi zargin cewa an dannen ƙuri’un jam’iyyar a zaɓen 2023.

“NNPP tana aiki sosai domin bayan zaben, mun gano cewa an danne mana kuri’u. Sama da miliyan biyar na kuri’unmu aka danne,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *