Friday, May 30
Shadow

Atiku ya soki EFCC kan tsare Hon Gudaji Kazaure

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC kan tsare tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Muhammad Gudaji Kazaure.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya kwatanta kama Kazaure da kuma tsare shi a matsayin saɓa wa doka.

“EFCC ta sake aikata abin da ta saba na take doka, ta hanyar kamawa da kuma tsare ƴan ƙasa da ba su aikata laifin komai ba,” in ji Atiku.

Ya yi misali da labarin fitattcen ɗan gwagwarmayar nan Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da Verydarkman wanda EFCC ta kama amma ta sake shi bayan matsin lamba daga wajen ƴan ƙasar.

Karanta Wannan  An yi jana'izar mutanen da harin jirgi ya kashe bisa kuskure a Zamfara

“Yanzu kuma hukumar ta koma kan Gudaji Kazaure. Sun kama shi ba tare yin wani bayani na laifi da suke tuhumarsa da aikatawa ba.

“An ɗauke shi daga Kano zuwa Abuja, kuma har yanzu babu wani bayani da EFCC ta yi wa iyalansa da kuma ƴan Najeriya,” a cewar Atiku.

Ya ce ko da akwai abin da mutum ya aikata – to ya kamata a bi hanyar shari’a wajen gurfanar da shi.

“Hakkin hukumar ne ta fito ta yi wa jama’a bayani kan abin da ya sa ta kama Kazaure, kuma bai kamata su riƙa tsare mutane da sunan yin bincike ba.

Karanta Wannan  Trump ya yi barazanar kara wa China harajin kashi 100

“Ƴan Najeriya sun zuba ido suna kallo. Kuma tarihi ba zai manta ba,” in ji Wazirin na Adamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *