Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Yanda wani mutum da ya saci kaji da da awaki ya koma yana kukan awaki da charar kaji, da kanshi ya kai kanshi ofishin ‘yansanda inda yace a roki me awakin ya maidoshi daidai

Kalli Bidiyo: Yanda wani mutum da ya saci kaji da da awaki ya koma yana kukan awaki da charar kaji, da kanshi ya kai kanshi ofishin ‘yansanda inda yace a roki me awakin ya maidoshi daidai

Duk Labarai
Wani mutum dake aiki a gidan gona, ya yiwa me gidansa satar awaki biyu da kaji biyu. Saidai abin mamaki shine ya tsere garin Mombasa sai ya rika kukan awaki da carar kaji. Da yawa dai sun yi amannar cewa, Asiri me gonar ya masa. Mutumin dai da kanshi ya kai kanshi ofishin 'yansanda. https://www.youtube.com/watch?v=kdvFEmVb6aA?si=1AkrGCZBURMsd5wS Sunan wanda yayi satar Baraka Joseph kuma dan ahekaru 16 ne. https://twitter.com/chude__/status/1946863679988781152?t=SOi_q_RHhieE790xz-jQ7A&s=19 Abin ya baiwa mutane mamaki sosai.

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Najeriya>>Inji Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMET

Duk Labarai
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da hasashen yanayi na kwana uku, daga Litinin 21 zuwa Laraba 23 ga Yulin 2025, inda ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar. A kan haka NiMet ta shawarci al'umma da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar samun ambaliya da kuma ɓarna da iska mai ƙarfi ke iya haddasawa. A cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafin sada zumunta na X, jihohin Arewa da na Kudu da kuma yankin tsakiya, duk za su fuskanci iska mai ƙarfi haɗe da ruwan sama. Hasashen ya nuna cewa a ranar Litinin da safe, za a samu ruwan sama da iska a jihohin Taraba da Adamawa da Kebbi da Borno da Yobe da Gombe da Bauchi da Sokoto da Kaduna. Ya kuma nuna cewa yankin tsakiyar ƙasar kamar Abuja da Naija da Plateau da Nasarawa d...
Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin ‘Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja

Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin ‘Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Mun Dauki Tsawon Shekaru Talatin Muna Aiki Ba Dare Ba Rana, Amma Yanzu Hakkiñmu Ya Gagara Fita Da Za Mu Ciyar Da Iyalanmu, Cewar Tsoffin 'Yan Sandan Nijeriya Dake Zañgà-Zañgà A Abuja
DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

Duk Labarai
Daga Muhammad Kwairi Waziri Mohammed Babangida, ɗan tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi watsi da nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya masa a matsayin Shugaban Bankin Manoma na Najeriya (BOA). Majiyoyi sun tabbatar da cewa Mohammed ya bayyana rashin amincewarsa da muƙamin, yana mai cewa wasu dalilai na sirri da kuma tsare-tsaren kansa ne suka sa ya yanke shawarar kin karɓa, duk da girmansa. Nadin nasa ya kasance cikin jerin sabbin nade-naden da shugaban ƙasa ke yi domin farfaɗo da harkokin noma da bunkasa rayuwar manoma a ƙasar nan. Sai dai wannan mataki da Mohammed ya ɗauka na watsi da mukamin ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da cikin ‘yan siyasa. Har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa ko daga bakin Mohammed Baban...
Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Maitama Abuja ta hana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello Fasfo dinsa dan ya je kasar waje neman magani. Mai shari'a Justice Emeka Nwite ya bayyana wannan hukunci. Yace takardun da Tsohon gwamnan ya gabatar na neman ya tafi kasar ingila basu da tambarin sarki wanda kotun tace basu da wani amfani a wajanta. Dan haka tace kuma rashin lafiyar ta tsohon gwamnan ba ta yi tsananin da za'a ce sai an fitar dashi kasar waje ba. Ana zargin tsohon gwamnan da dan uwansa, Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu wajan satar Naira N80, 246,470, 088.88.
Da gaske an soke jarabawar WAEC ta 2025 saboda yawan satar amsa? Hukumar jarabawar ta yi karin bayani

Da gaske an soke jarabawar WAEC ta 2025 saboda yawan satar amsa? Hukumar jarabawar ta yi karin bayani

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta WAEC ta yi martani kan labarin da ke cewa an soke jarabawar ta shekarar 2025. Labarai na ta jawo a kafafen sadarwa inda aka ji wasu na cewa an soke jarabawar ta shekarar 2025. An bayyana cewa an soke jarabawar ne saboda yawaitar satar amsa. Saidai hukumar ta WAEC a Martani kan lamarin tace bata soke jarabawar ba asali ma nan da watan Augusta zata saki sakamakon jarabawar. “The attention of the West African Examinations Council (WAEC), Nigeria, has been drawn to a press statement alleging the cancellation of all the papers written during the just concluded WASSCE for School Candidates, 2025. According to the press statement dated Saturday, July 19, 2025, being circulated on social media platforms, the Federal Ministry of Education, ...
Kotu ta daure mutane 2 a gidan yari saboda sare itace a Kano

Kotu ta daure mutane 2 a gidan yari saboda sare itace a Kano

Duk Labarai
Kotu dake Normansland a Kano ta daure mutane 2 bisa hannu a sare itace a jihar wanda sabawa dokar Muhalli ta jihar ne. Ma'aikatar Muhalli ta jihar, ta sanar da cewa an kama wani me suna Salihu Mukhtar da wani abokin aikinsa da suka sare itace akan titin Jigawa Road dake Nasarawa GRA. Lauya me gabatar da kara, Barrister Bahijjah Aliyu ne ya gayawa kotu cewa wadanda aka kama din sun karya dokar muhalli ta jihar. An yankewa daya daga cikinsu hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari ko biyan tarar Naira 20,000. Sannan aka yankewa dayan hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari ko biyan tarar Naira dubu 50. Kwamishinan muhalli na jihar, Dr. Dahiru Hashim ya bayyana cewa ba zasu amince da sare itatuwa a jihar ba.