An kàshè mutane 20 a sabbin hàrè-hàrèn da aka kai jihar Filato
Hare-haren da aka kai a Jihar Filato sun hallaka aƙalla mutum 20 a wannan makon, in ji majiyoyin gwamnati da ƙungiyoyin agaji a ranar Laraba.
Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin.
Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar Mangu a ranar Litinin da Talata, sun biyo bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya da ake kyautata zaton sun fara ne yayin da mutane ke aikin haƙar ma’adinai a yankin da ke da arzikin Tin, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, da ya shaida wa Kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Makiyayan Fulani Musulmai masu yawo da dabbobi sun daɗe suna samun saɓani da manoma da suke zauna a Jihar Filato — waɗanda mafi yawansu Kiristoci ne — kan rikicin mallakar fili da albarkatun ƙasa...








