Tinubu Akwai Zalamar Mulki, Yanzu duk wahalar rayuwa da matsalar tsaro da sauransu da ‘yan Najeriya ke ciki bai dameshi ba, zarcewa akan kujerar mulki ce a gabanashi? Inji Jam’iyyar PRP
Daya daga cikin jam'iyyun adawa a Najeriya wato PRP, ta yi alawadai da amincewar da kwamitin zartarwa na kasa na jam'iyyar APC mai mulki, da gwamnonin jam'iyyar, da 'yan majalisar dokoki na kasa na jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki suka yi wa shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu, domin ya sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara ta 2027.
Jam'iyyar PRP ta bayyana fargabar, cewa wannan mataki wata zalamar mulki ce kawai, wadda ta fayyace aniyar jam'iyyar APC ta neman ci gaba da mulki karfi da yaji ta hanyar wani goyon baya na musamman da aka tsara, maimakon a bari jama'ar kasa su bayyana ra'ayinsu game da takarar shugaban kasar a zaben da ke tafe.
Kwamred Muhammed Ishak, shi ne sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PRP, ya shaida wa BBC cewa sanin kowa ne ba wani dad...








