Monday, March 30
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Fadan Shugaba Tinubu da Gwamnan Legas: Ji yanda ta kaya

Fadan Shugaba Tinubu da Gwamnan Legas: Ji yanda ta kaya

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Legas na cewa, Fadan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da gwamna Legas, Babajide Sonwo Olu ya zo karshe. Gwamnan legas din ya musanta zargin cewa akwai wata rashin Jituwa a tsakaninsa da Tinubu inda yace Tinubu ubane sannan kuma shugabansa ne. Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a Legas din bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasar Ranar Lahadi inda yace dama can babu wata rashin Jituwa a tsakaninsu. An yi ganawar ne a gidan shugaban kasar dake Ikoyi. An fara zargin akwai wata kullalla tsakanin shugaba Tinubu da Gwamna Sonwo Olu ne bayan da shugaban ya kaddamar da Titin Legas zuwa Calabar amma ba'a ga Sonwo Olu a wajan ba. Sannan a wajan wani taro, shugaban ya gaisar da kowa dake wajan amma bai gaishe da gwamnan Legas din ba.
Ana zargin an baiwa wasu ‘yan Jam’iyyar APC Mukami a hukumar zabe dan su taimakawa Shugaba Tinubu ya ci zaben 2027

Ana zargin an baiwa wasu ‘yan Jam’iyyar APC Mukami a hukumar zabe dan su taimakawa Shugaba Tinubu ya ci zaben 2027

Duk Labarai
Rahotanni na cewa, ana zargin an baiwa wasu 'yan jam'iyyar APC mukami a hukumar zabe me zaman kanta, INEC dan su taimakawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yaci zabe. Kungiyar fafutuka dake saka ido kan yanda akw gudanar da Gwamnati me suna SERAP ce ta yi wannan zargi inda tace tana neman shugaban kasar da ya duba wannan zargi da ake idan gaskiyane a cire wadannan mutane. SERAP tace kamata yayi a maye wadannan mutane da 'yan kasa na gari masu kishi wadanda basu da alaka da kowace jam'iyya. Mataimakin Darakta na SERAP, Kolawole Oluwadare ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ranar 7 ga watan Yuni inda yace barin wadannan mutane a cikin INEC zai sa mutuncin da ake ganin hukumar dashi da gaskiya ya zube. Wadanda ake zargin 'yan APC dinne dake aiki a hukumar INEC sune kamar ...
WANI DAN JAGALIYA YA CHÀKÀWÀ NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA

WANI DAN JAGALIYA YA CHÀKÀWÀ NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA

Duk Labarai
WANI DAN JAGALIYA YA CHAKAWA NI BABBAN SOJA WUKA HAR LAHIRA A GADAR KAWO TA JIHAR KADUNA. Rahotanni daga Jihar Kaduna sun tabbatar da cewar Wani babban jami’in soja, Laftanar Commodore M. Buba, ya rasa ransa bayan da wani ɓarawon waya ya soka masa wuƙa a ƙirji, Kuma ya rasa rayuwar sa har Lahira. Bala'in ya faru ne a gadar Kawo, lokacin da jami’in ya tsaya domin gyara tayar motarsa da ta fashe yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Jaji, inda yake karatu a Makarantar Horas da Sojoji ta Armed Forces Command and Staff College. Kakakin hukumar Yan'sanda ta kasa reshen Jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar da aukuwar lamarin. Shedun gani da Ido sun ce Sojan ya hana barawon wayar ne kamar yadda ya bukata tun da farko, shi Kuma barawon ya zare wuka ya soka masa a kirji. ...
Kalli Bidiyo: Ba’amurkiya ‘Yar shekaru 68 ta auri matashi dan shekaru 25 a Najeriya

Kalli Bidiyo: Ba’amurkiya ‘Yar shekaru 68 ta auri matashi dan shekaru 25 a Najeriya

Duk Labarai
Wata mata ba'amurkiya me shekaru 68 ta zo Najeriya ta auri matashi dan shskaru 25. Matar tace a shafin facebook suka hadu inda tace ya fara liking wani comment da ta yi ne inda daga nan suka fara magana. https://www.youtube.com/watch?v=CNCGYAsOv9g?si=yCtzO2upWK8DXlTD Tace ta taso daga kasarta tazo Najeriya suka hadu da masoyinta kuma yace yana sonta.
Shugaban Kwamitin Da’a na majalisar Dattijai zai bar jam’iyyar sa ta Labour Party zuwa APC

Shugaban Kwamitin Da’a na majalisar Dattijai zai bar jam’iyyar sa ta Labour Party zuwa APC

Duk Labarai
Shugaban Kwamitin Da'a na majalisar Dattijai, Senator Neda Imasuen, wanda ya fito daga jihar Edo zai bar jam'iyyarsa ta Labour party zuwa jam'iyyar APC. Rahotanni ya shirya tsaf dan canja jam'iyyar tasa. Ya bayyana cewa, zai dauki wannan mataki ne saboda jam'iyyarsa ta Labour party ta rasa Alkibla. Yace kuma zai sanar da komawarsa jam'iyyar APC ranar 12 ga watan Yuni a birnin Benin City.