Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta saka ranar Alhamis 24 ga watan Afrilu a matsayin ranar fara jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar, ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da kumar ta ce muhimman matakan da ta ɗauka da kuma dauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin.
Dr Fabian Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar - wadda ke ɗauke da muhimman bayanai dangane da jarrabawar.
Ya ƙara da cewa akwai bayanin wuri da lokacin mutum zai zana jarrabawar da sauran muhimman bayanai game da yadda tsarin zaman ɗakin jarrabawar zai kasance duka a jikin katin.
Dubban ...
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya roki yan siyasar Jihar Kano da su tuna irin zumuncin da ke tsakaninsu kada su bari banbancin ra'ayin siyasa ya raba kansu.
Kashim Shettima yayi wannan roko ne a gaban gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Shugaban jam'iyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas da sauran jiga jigan yan siyasa daga bangaren Kwankwasiyya da Gandujiyya a lokacin da yake ta'aziyar rasuwar Galadiman Kano marigayi Abbas Sunusi.
Kashim Shettima ya ce kuskure ne shiyasa a jiha kamar kano da ake takama da ita a kowanne mataki ta raba kan mutanan Kano ko kawo cikas a a tsakaninsu.
"Jihar Kano itace abar koyi a duk Najeriya,dan haka bama murna idan munga ana samun sabanin ra'ayin siyasa kuma ana nuna juna yatsa. Kano itace cibiyar Arewa ,duk abinda ya sha...
Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Auwal Muhammad Jatau ya yi magana akan rahoton dake cewa ya zabgawa ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar mari.
Jatau yayi magana ta bakin kakakinsa, Muslim Lawal inda yace rahoton marin ba gaskiya bane
Yace su basu ma da labari game da maganar marin a bakin 'yan jarida suke ji.
Yace babu ta yadda za'a yi mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya mari minista, yace ko gwamna ba zai mari minista ba ballantana mataimakinsa.
Kokarin jin ta bakin ministan ya ci tura.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Wani matashi dalibin jami'a a kasar Ghana ya kàshè kansa ta hanyar rataya bayan kama budurwarsa na cin amanarsa.
Lamarin ya farune a jami'ar University of Education, Winneba dake kasar ta Ghana ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu.
Saidai ba'a bayyana sunan dalibin ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin ya yanke jiki ya fadi bayan kama budurwar tasa inda kuma daga bisani ya shiga daki ya rataye kansa.
'Yansandan garin Winneba sun dauke gawar matashin inda suka tafi da ita suka...
A ranar Juma’a ne wani Al'amari mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a fadar Sarkin Bauchi, inda aka zargi mataimakin gwamnan jihar Auwal Jatau da Zabgawa ministan harkokin kasashen Waje Yusuf Maitama Tuggar Mari a Sa'ilin da wata hatsaniya mai zafi ta barke Tsakannin Ministan Da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake bikin nada tsohon gwamnan jihar Bauchi, Barrista Mohammed Abdullahi Abubakar, a matsayin Makama Babba na Masarautar Bauchi, wanda ya yi daidai da daurin auren diyarsa, Khadija Mohammed.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan yan siyasa da suka hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima,da gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da dai sauransu.
A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya samo asali ne bayan da rahotanni suka ce minist...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayarwa da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Datti Baba Ahmad martani bayan da yace idan shugaban kasar na da wayau kada ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 saboda faduwa zabe zai yi.
A martaninsa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace maganar Datti ta banza ce wadda ba basira ko kadan a ciki.
Da yake magana da bakin kakakinsa, Daniel Bwala, Shugaba Tinubu yace Datti Ahmad ya daina shiga harkar da bai iya ba, watau siyasa, ya barwa wanda suka iya su yi.
Yace yayi kokari sosai na daukar matakan gyara wanda 'yan Najeriya sun shaida kuma har kungiyoyin Duniya irin su IMF sun jinjina masa inda suka ce ya Dora Najeriya a turbar karfafa tattalin arziki.
Ministan babban birnin Tarayya Abuja, Nyesome Wike ya bayyana cewa babu dan Arewar da ya isa ya zama shugaban kasa sai a shekarar 2031 bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gama wa'adinsa karo na biyu.
Ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja.
Wike yace dan Arewa ya yi mulki har sau biyu dan haka Shima Tinubu sai yayi sau biyu daga kudu kamin wani dan Arewa ya sake mulka.
Yace babu wani yanki da zaice shi kadai zai ta yin mulkin Najeriya, tsarin karba-karba za'a ci gaba da yi.
Sojan Najeriya da ya ajiye aiki sannan ya samu aiki da hukumar sojin kasar Rasha ya sanar da cewa ya tafi kuma yana bukatar addu'ar 'yan Najeriya.
Sojan ya nuna hotunansa a yayin da yake filin jirgin sama dan tafiya kasar ta Rasha.
Yace yana bukatar addu'a