Saturday, March 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo: Wata Sabuwar Masifa ta Shigo kafafen sada zumuntar Arewa inda ake cin zarafin malamai ta hanyar Amfani da AI asa su yi rawa

Kalli Bidiyo: Wata Sabuwar Masifa ta Shigo kafafen sada zumuntar Arewa inda ake cin zarafin malamai ta hanyar Amfani da AI asa su yi rawa

Duk Labarai
Wata sabuwar masifa da ta shigo kafafen sada zumuntar Arewa itace ta amfani da wani AI ana saka hotunan malamai ana sawa su yi rawa. Wannan AI a baya 'yan siyasa kawai akewa amfani dashi amma yanzu lamarin ya kai har kan malamai. https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7494342086968462647?_t=ZM-8vmO2enRDGw&_r=1 Wasu daga cikin Malam da muka ci karo an yi Amfani da wannan AI din an sa sun yi rawa sun hada da Marigayi Shaikh Jafar Adam, da Sheikh Bala Lau da Sheikh Maqari. https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7495429012479659319?_t=ZM-8vmO9SppUg9&_r=1 Wani abin takaici ma shine lamarin ya koma gasa tsakanin matasa mabiya akidu, idan wannan ta saka malamin wannan akida rawa, sai shima wancan ya rama. https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7494...
Kalli Bidiyon mummunar girgizar kasar data faru a kasar Turkiyya, mutane na ta gudun ceton rai

Kalli Bidiyon mummunar girgizar kasar data faru a kasar Turkiyya, mutane na ta gudun ceton rai

Duk Labarai
Aƙalla mutane 151 ne suka samu raunuka bayan sun durgo daga dogayen gine-gine saboda tsoron da girgizar ƙasa ta haifar, a cewar ofishin gwamnan Istanbul. https://www.tiktok.com/@live_news00/video/7496509730362281238?_t=ZM-8vmJNkmOYiL&_r=1 Ofishin ya kuma wallafa a shafinsa na X, cewa ba a samu asarar rayuka ba, kuma babu wani gini da mutane ke zaune a ciki da ya ruguje. Sai dai wani gini wanda babu kowa a ciki ya ruguje sakamakon girgizar ƙasar. https://twitter.com/The_NewArab/status/1915025667365683236?t=7ep6E-k1HezvWfbB4qwjPQ&s=19 Ministan ilimi na Turkiyya, Yusuf Tekin ya sanar da cewa za a rufe makarantu na kwana biyu Alhamis da Juma'a. Aƙalla an samu girgiza sau 51 a birnin a ranar Laraba, inda mafi girmansu ya kai ƙarfin maki 6.2, wanda ya shafi Istambul...
Akwai ƴanƙasar waje da ke kai hari a Benue – Alia

Akwai ƴanƙasar waje da ke kai hari a Benue – Alia

Duk Labarai
Gwamnan jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya, Hyacinth Alia ya yi zargi cewa maharan da suka kai hari jihar ba ƴan Najeriya ba ne. Gwamnan ya faɗi hakan ne a wani shirin gidan talbijin na Channels, inda ya ce maharan na magana ne da wata irin Hausa da Fulatanci wanda ba irinsu ake yi a ƙasar ba. "Waɗannan mutanen sun zo ne a shirye da makamansu da bindigogi ƙirar AK-47 da 49. Kuma ba su yi kama da ƴan Najeriya ba, ba sa magana kamar yadda muke yi, Hausarsu ba irin ta mu ba ce. " Inda ya ƙara da cewa daga bayanan sirrin da suka samu daga mazauna yankunan da aka kai hare-hare, ya nuna cewa maharan ƴanƙsar waje ne. Hakan na zuwa ne bayan wata ziyarar nuna alhini da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya kai jihar. Inda ya bai wa al'umomin jihar ta...
Gwamnatin Kaduna ta ƙwace gidajen da El-Rufa’i ya sayar

Gwamnatin Kaduna ta ƙwace gidajen da El-Rufa’i ya sayar

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Uba Sani ya bayar da umarnin ƙwace gidaje da filayen da tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta Malam Nasiru El-Rufa'i ta sayar a jihar. Gidajen da filayen da aka ƙwacen sun haɗa da waɗanda tsohon gwamnan ya sayar a kwalejin Queen Amina da ke Kaduna da kwalejin Alhuda-huda da kwalejin Government Commercial da ke Zaria. Umarnin na ƙunshe ne a wata sanarwar da aka fitar, a ranar Talata da daddare, mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Dr AbdulKadir Mu’azu Meyere. Sanarwar ta bayyana cewa an ƙwace gidajen da filayen ne saboda amfanin al'umma. Sai dai an jima ana takun saƙa tsakanin gwamna Uba Sani mai ci yanzu, da kuma wanda ya gada, Malam Nasir El-Rufa'i.
Ya kamata shuwagabannin Najeriya su yi koyi da halin  marigayi Fafaroma na son Talakawa>>Inji Jam’iyyar NNPP

Ya kamata shuwagabannin Najeriya su yi koyi da halin marigayi Fafaroma na son Talakawa>>Inji Jam’iyyar NNPP

Duk Labarai
Wanda ya kirkiro jam'iyyar NNPP, Boniface Aniebonam ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yi koyi da halin Marigayi Fafaroma Francis na son Talakawa. Ya bayyana hakane a sakonsa na ta'aziyyar fafaroman inda yace babu ta yanda za'a yi a ci gaba da barin wagegen gibin dake tsakanin Talakawa da masu kudi yana kara karuwa amma ace ana son zaman Lafiya. Yace dolene Gwamnati ta mayar da hankali wajan yaki da Talauci kuma hakan ba aikin gwamnati ne kadai ba hadda masu hannu da shuni.
Ba bÒm bane ya tashi a Kaduna, Bindiga hadin gidace ta tashi ba da shiri ba

Ba bÒm bane ya tashi a Kaduna, Bindiga hadin gidace ta tashi ba da shiri ba

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi karin haske kan rahotannin dake cewa Bam ya fashe a Unguwar Abakpa dake jihar. A jiya ne dai rahotanni suka rika yawo cewa Bam din ya fashe ne inda har ya kashe yara biyu da jikkata wasu mutane 3, Kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Saidai a jawabin da gwamnatin jihar ta fitar ta bakin Kwamishinan tsaron cikin gida, Sir James A. Kanyip, KSM; PhD tace rahoton ba gaskiya bane. Yace abinda ya faru shine, Bindiga hadin gida ce ta tashi ba tare da shiri ba shine abinda ya faru. Yace Tuni jami'an tsaro suka kai dauki wajan da abin ya faru sannan ana kan bincike.
Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja.

Duk Labarai
Daga Yau Duk Wanda Kuka Gani Namiji Da Kitso Ko Dada Ku Kamashi Ku Datse Kuma Kuyi Mashi Tara….. Gwamnan Jihar Neja. Gwamnan jihar Neja Manomi Umaru Mohammed Bago ya ayyana sababbin dokoki da zasu fara aiki nan take a faɗin jihar. Gwamnatin jihar ta Neja ta haramta bangar siyasa da duk wani abu mai kama da haka a faɗin jihar. Duk wanda aka same shi da wani makami da ya haɗa da wuka ko sanda a ɗauke shi a matsayin Ɗan fashi da makami, idan kuma yayin gardama da jami'an tsaro aka harbe shi da harsashen bindiga kada abada shi har sai ƴan uwan shi sun biya kuɗin wannan harsashen da akayi asarar shi. Duk wanda aka gani namiji da kitso ko Dada akan shi a kama shi a kuma aske kan. An Haramta amfani da Mashi mai ƙafa Biyu da mai ƙafa Ukku Keke Napepe daga ƙarfe Shidda na Yamma ...