Kaso 90 cikin 100 na Kiristocin da ake ķķàshèwà a Duniya a Najeriya ake ķķàshèsu, Najeriya ta kasa baiwa Kiristoci kariya dan haka zamu Kakaba mata Takunkumi>>Inji Kasar Amurka
Majalisar kasar Amurka ta baiwa shugaban kasar, Donald Trump shawarar ya kakabawa Najeriya takunkumi saboda yawan kashe kiristoci da ake yi a kasar.
Majalisar ta cimma wannan matsayane bayan samun bayanai daga wani bincike da aka gudanar da yake nuna cewa kaso 90 na kiristocin da ake kashewa a Duniya a Najeriya ne hakan ke faruwa.
Majalisar ta kasar Amurka ta zargi Najeriya da kasa daukar matakan da suka kamata dan baiwa Kiristocin kariya daga hare-haren ta'addanci dake yin sanadiyyar mutuwarsu.
Saidai a martanin Gwamnatin Najeriya tace wannan magana ba gaskiya bace.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ta fitar ta hannun kakakinta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya bayyana cewa, tabbas akwai matsalar tsaro a Najeriya.
Amma ba wani addini daya aka ware shi k...








