Tuesday, February 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Duk Labarai
Wani magidanci a kasar Afrika ta kudu ya saki matarsa biyo bayan sumbatarta da mawakin kasar Amurka, Chris Brown yayi. Mutumin me suna Lusaka dan kimanin shekaru 42 ya gamu da takaici ne bayan ganin hotunan sumbatar matarsa da Chris Brown din yayi. Kwanannan dai Chris Brown din ya je kasar Afrika ta kudu inda yayi wasa sannan kuma ya gana da masoyansa inda a canne ya hadu da matar me shekaru 34. Mijin yace abinda matar ta aikata rashin girmamashi ne kuma ya yiwa aurensu bacin da ba zai gyaru ba. Yace kuma abinda matar ta yi bai kamata ace matar aure ta aikata hakan ba. Mijin dai yawa matar magana dan ya mata fada amma sai ta gaya masa cewa, wannan ba wani abin tada hankali bane.
Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar mayar da sabis karɓa-karɓa

Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar mayar da sabis karɓa-karɓa

Duk Labarai
Ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriya ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar katsewar network matuƙar ba a sauya tsarin yadda suke cajar kuɗaɗe a fannin sadarwa ba duk da yadda suke gudanar da ayyukansu ke ƙara tsada. Shugaban ƙungiyar masu kamfanonin sadarwa da ke da lasisi a Najeriya Gbenga Adebayo ne ya bayyana hakan a yau Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ɓangaren sadarwa na tsaka maki wuya saboda tashin gauron zabi da ake fuskanta sakamakon tashin farashin kayayyaki, da rashin tabbas a kasuwar musayar kudi da kuma tashin farashin makamashi. Cikin sanarwar Mista Adebayo yace duk da ƙalubalen da ake fuskanta na gudanarwa, har yanzu ba su ƙara kuɗaɗen da suke cajar mutane ba, wani abu da yake barin masu kamfanonin cikin mawuyacin hali wajen kiyaye ingancin aikin d...
Alhamdu Lillah Addinin Musulunci ya samu ƙaruwa, wata budurwa ƴar kimanin shekaru 16 ƴar ƙabilar Igbo ta karɓi addinin Musulunci da sanyin safiya, ta canza suna zuma Maryam

Alhamdu Lillah Addinin Musulunci ya samu ƙaruwa, wata budurwa ƴar kimanin shekaru 16 ƴar ƙabilar Igbo ta karɓi addinin Musulunci da sanyin safiya, ta canza suna zuma Maryam

Duk Labarai
Alhamdu Lillah Addinin Musulunci ya samu ƙaruwa, wata budurwa ƴar kimanin shekaru 16 ƴar ƙabilar Igbo ta karɓi addinin Musulunci da sanyin safiya, ta canza suna zuma Maryam. Kuma tace ba zata iya komawa gidan su ba saboda suna iya kashe ta, don haka ana neman wanda zai aure ta ya riƙe ta tare da koyar da ita addinin Musulunci. Don Allah ana roƙon ƴan'uwa al'ummar Musulmi duk wanda yaci karo da wannan labarin ya taima wajen tura shi zuwa sauran groups ko Allah zai sa a samu wanda zai iya riƙe ta bisa amana
Ka Yi Gaggawar Janye Kalamanka Kan Dokar Haraji Domin Zai Tada Hankulan ‘Yan Kasa, Umarnin Fadar Shugaban Kasa Ga Gwamnan Bauchi

Ka Yi Gaggawar Janye Kalamanka Kan Dokar Haraji Domin Zai Tada Hankulan ‘Yan Kasa, Umarnin Fadar Shugaban Kasa Ga Gwamnan Bauchi

Duk Labarai
Ka Yi Gaggawar Janye Kalamanka Kan Dokar Haraji Domin Zai Tada Hankulan 'Yan Kasa, Umarnin Fadar Shugaban Kasa Ga Gwamnan Bauchi Gwamnatin tarayya ta ayyana kalaman Gwaman jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, a matsayin kalaman tada hankulan 'yan kasa kan dokar fasalin haraji. Mai magana da yawun Shugaban kasa ne Sunday Dare, ne ya bayyana a shafin sa na twitter a safiyar yau Litinin. Daga Muhamma kwairi Waziri
YANZU YANZU: Hukumar DSS ta fara kama mutanen da suke ɗora Bidiyon Sojojin ƙasar Faransa da suke a Nigeria a kafafan Sada Zumunta, inda Yanzu haka Jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun cafke ɗan gwagwarmaya Mahadi Shehu, bisa zargin yaɗa bidiyon Sojojin Faransa a shafinsa na X, da ke nuna cewa akwai masaukinsu a Nijeriya

YANZU YANZU: Hukumar DSS ta fara kama mutanen da suke ɗora Bidiyon Sojojin ƙasar Faransa da suke a Nigeria a kafafan Sada Zumunta, inda Yanzu haka Jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun cafke ɗan gwagwarmaya Mahadi Shehu, bisa zargin yaɗa bidiyon Sojojin Faransa a shafinsa na X, da ke nuna cewa akwai masaukinsu a Nijeriya

Duk Labarai
DSS Ta Kama Mahdi Shehu Saboda yada Bidiyon sojojin Faransa. Hukumar tsaro ta farin kaya ta (DSS) ta kama Mahdi Shehu, mai fafutuka kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa daga Kaduna. An Kama shi ne biyo bayan zargin da ake yi masa na yaɗa bidiyon sojojin Faransa a shafinsa na X. A cewar rahotanni, bidiyon ya nuna Shehu yana ikirarin cewa gwamnatin Najeriya tana shirin kafa sansanin sojojin Faransa a yankin Arewa maso Yamma, ikirarin da aka musanta. Mahdi yana hannun DSS a Kaduna, kuma akwai yiwuwar a gurfanar da shi a gaban kotu nan ba da jimawa ba. Hukumar DSS ta bayyana cewa sun tattauna da Mahdi kan rashin ingancin bayanan bidiyon kafin kama shi, amma tattaunawar ba ta kai ga nasara ba. Duk da haka, an umarci jami’an tsaro su mutunta haƙƙinsa yayin tsare shi.
Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna

Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna

Duk Labarai
Shugaba Buhari ya ce ba zai rubuta takarda ba kamar yadda sauran Shuwagabanni ke yi saboda gudun kada ya ɓatawa wasu mutane da iyalansu suna Mista Buhari ya ce ba zai yiwu ya rubuta takarda ba tare da ya ambaci sunayen wasu mutane ba wanda hakan ka iya jawo masu ɓacin rai ko bacin suna Me zaku ce?

Maganin yawan fushi

Magunguna
Yawan fushi matsala ce wadda idan mutum na da ita, zai yi fama da ma'amala da mutane. A wannan rubutu, zamu yi bayani dalla-dalla kan maganin yawan fushi dan kaucewa aikin dana sani. Idan kana da yawan Fushi, kada ka zama me yawan magana. Musamman a yayin da ranka ya baci, idan kace zaka yi magana, zaka yi dana sani akan abinda ka fada. Ka yi tunani, ko ka bari ka huce kamin kace wani abu, shima wanda ya maka ba daidai ba, ka barshi ya dawo hayyacinsa tukunna. Masana kiwon Lafiya sun bayyana cewa, idan ka yi fushi sosai, kuma ka kasa shawo kanka, to ka je ka motsa jiki, kamar tafiya da sauri ko yin gudu. Idan zai yiyu, ka samu guri kai kadai ka zauna ka nutsu na dan mintuna. Idan kai musulmi ne ka yawaita ziki, da karatun Qur'ani, zaka samu saukin lamarin. Hakanan idan a...
Tawagar Gwamna Ta yi hadari

Tawagar Gwamna Ta yi hadari

Duk Labarai
Tawagar Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ta yi hadari a garin Ihugh dake karamar hukumar Vandeikya dake jihar Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Lamari ya farune ranar Lahadi inda shaidun gani da ido suka ce daya daga cikin motocin tawagar gwamnan ce ta buge wani mutum ya mutu. Lamarin ya farune yayin da gwamnan ya je gida yin hutun bikin kirsimeti. Lamarin ya faru sau biyu ne a yayin da gwamnan ke zuwa gida da lokacin da yake dawowa. Saidai me magana da yawun gwamnan, Solomon Iorpev ya musanta faruwar hadarin da tawagar gwaman, yace mota daya ce wadda aka bari a baya sauran motocin tawagar gwamnan sun wuce ta yi hadarin. An tuntubi kakakin 'yansandan jihar,  SP Catherine Anene, saidai bata ce komai akan lamarin ba.