Sunday, March 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kan sojojinta a jihar Borno. A wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce an kashe sojoji guda shida, sannan wani kwamandan ƴan sa-kai ya jikkata. Sai dai Buba ya ƙara da cewa a gumurzun, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan Boko Haram 34, sannan sun ƙwato wasu makamai. Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya. A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar da ke jihar Borno.
An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

An kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus na naira 77,000 — NYSC

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ce an kusa fara biyan masu yi wa ƙasar hidima alawus na naira 77,000 da aka amince za a riƙa biyansu na wata-wata. Darakta-janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana haka a ranar Talata a wata sanarwa da kakakin NYSC, Caroline Embu ta fitar kamar yadda tashar Channels ta ruwaito. Ahmed ya ce zai mayar da hankali kan jin daɗin masu yi wa ƙasa hidima, inda ya ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun kammala domin fara biyan sabon alawus ɗin. An dai ƙara alawus ɗin ne tun bayan da gwamnatin Najeriya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata a ƙasar.
Ana barazanar kkasheni saboda na yi magana akan Peter Obi>>Inji Me magana da yawun APC, Felix Morka

Ana barazanar kkasheni saboda na yi magana akan Peter Obi>>Inji Me magana da yawun APC, Felix Morka

Duk Labarai
Me magana da yawun Jam'iyyar APC, Felix Morka ya bayyana cewa, an aika masa barazanar kisa har guda 400 wanda daga ciki guda 200 kai tsaye aka ce za'a kasheshi ko yankashi saboda yayi magana akan Peter Obi. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV inda yace an masa kazafin cewa ya yiwa rayuwar Peter Obi Barazana. Yace shi karya ake masa, babu inda yawa rayuwar Peter Obi Barazana. Yace tuni aka fara kaiwa wasu daga cikin 'yan uwansa hari inda yace ya dauki bayanai akan wannan barazana da ake masa inda zai kaiwa hukumar 'yansanda korafi. A baya dai, Shima Peter Obi yace ana yiwa rayuwarsa barazana.
Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Gidan Yari Na Jihar Katsina Ya Ziyarci Buhari Bayan Ya Karbi Ragamar Kama Aiki

Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Gidan Yari Na Jihar Katsina Ya Ziyarci Buhari Bayan Ya Karbi Ragamar Kama Aiki

Duk Labarai
Daga Comr Nura Siniya Tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammad Buhari, ya karɓi baƙuncin sabon shugaban ma'aikatan hukumar kula da gidan gyaran hali na jihar Katsina Mr. Umar Baba, a gidansa na Daura dake jihar Katsina Sabon Kwantirolan NIS Umar Baba, ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, a ranar 7 ga Janairu, 2025.
Farashin kayan Abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoman Arewa sun zabi kai kayan amfanin gonarsu kasashen waje

Farashin kayan Abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoman Arewa sun zabi kai kayan amfanin gonarsu kasashen waje

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa ana hasashen farashin kayan abinci zai yi tashin gwauron zabi saboda manoma a Arewa sun zabin kai kayan abincinsu kasashen waje su sayar maimakon sayarwa a gida Najeriya. Manoma a jihohin Kaduna da Kwara sun koka da rashin amfanin gona me kyau saboda karancin ruwan sama da krkatar da kayan noman da 'yan siyasa suka yi. Saidai manoma a jihohin Jigawa, Kano da Yobe sun bayyana samun amfanin noma sosai irinsu Dawa, Wake, Masara, Gero da Sauransu. Saidai sun bayyana cewa, mafi yawancin kayan amfanin nasu zasu kaisu jihohin wajene dan sayarwa. Hakan a binciken jaridar Punchng ya nuna cewa, zai iya kaiwa ga hauhawar farashin kayan abinci a wannan shekarar.
Shugaba Tinubu ya canja ra’ayi kan maganar sauya Fasalin Haraji

Shugaba Tinubu ya canja ra’ayi kan maganar sauya Fasalin Haraji

Duk Labarai
Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar sadarwa, Daniel Bwala ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai iya la'akari da wasu sharuda daga gwamnoni akan maganar canja fasalin harajin kasa. Kudirin dokar canja karba da raba harajin wanda ke gaban majalisar tarayya ta fuskanci koma bayan da rashin karbuwa musamman ga gwamnonin Arewa inda hakan yasa dole majalisar ta dakatar da zartar dashi inda a yanzu ake bi dan jin ra"ayin jama'a. Duk da sukar da wannan kudirin canja haraji ke fuskanta, shugaba Bola Ahmad Tinubu ya jajirce akan cewa babu gudu ba ja da baya kan lamarin. Bwala a yayin hira da gidan talabijin na ChannelsTV ya bayyana cewa, maganar kudirin dokar canja fasalin haraji babu gudu ba ja da baya kuma majalisa zata amince da kudirin. Yace abinda gwamno...
Hotuna: Yadda dan gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kammala digiri na biyu a Jami’ar kasar Ingila, Inda ya karanci fannin shari’a. Ministan ne ya wallafa hakan a shafinsa na X, inda yake alfahari da hakan

Hotuna: Yadda dan gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kammala digiri na biyu a Jami’ar kasar Ingila, Inda ya karanci fannin shari’a. Ministan ne ya wallafa hakan a shafinsa na X, inda yake alfahari da hakan

Duk Labarai
Yadda dan gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kammala digiri na biyu a Jami'ar kasar Ingila, Inda ya karanci fannin shari'a. Ministan ne ya wallafa hakan a shafinsa na X, inda yake alfahari da hakan. Nyesom Wike
An saki Mubarak Bala, ɗan Najeriyar nan da ya yi suna wajen sukar addini bayan shafe shekara huɗu tsare a gidan yari kan tuhume-tuhumen da suka shafi ɓatanci ga addini

An saki Mubarak Bala, ɗan Najeriyar nan da ya yi suna wajen sukar addini bayan shafe shekara huɗu tsare a gidan yari kan tuhume-tuhumen da suka shafi ɓatanci ga addini

Duk Labarai
Ya shaida wa BBC irin ƙalubalen da masu aƙida irin tasa ta rashin yadda da kowane addini ke fuskanta. Mubarak Bala, shugaban kungiyar Humanist Association of Nigeria kuma fitaccen mai ikirarin rashin addini, ya samu 'yanci bayan shafe shekaru huɗu a gidan yari kan zargin batanci. An yanke masa hukuncin shekara 24 a kurkuku tun a fari a shekarar 2022, bayan ya amsa laifuka 18 da suka haɗa da batanci, tayar da zaune tsaye, da cin zarafin addini ta kafar sada zumunta. Hukuncin ya samo asali ne daga wallafa ra'ayoyinsa na sukar addinin Islama, Allah, da Annabi Muhammad (SAW) ta kafar sada zumunta, wanda ya haifar da fushin al'umma. Kafin a yanke masa hukunci, Mubarak ya yi shekara biyu yana jiran shari’a a tsare tun bayan kamashi a Kaduna a ranar 28 ga Afrilu, 2020. A cewar rahoton BB...
Adawa tsakanin tsofaffin gwamnoni na mayar da Kano baya – Garo

Adawa tsakanin tsofaffin gwamnoni na mayar da Kano baya – Garo

Duk Labarai
Tsohon ɗantakarar mataimakin gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo ya ce adawar siyasar da ke tsakanin tsofaffin gwamnoni na hana jihar ci gaba. Garo ya kuma yi kira ga jagororin siyasar jihar su mayar da kubensu, tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ciyar da jiharsu gaba. Garo ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ya ce, "babu daɗi ganin jihohi irin Zamfara da ba ta kai Kano ba, tsofaffin gwamnoninta suna ajiye bambancin siyasa suna haɗuwa domin ciyar da jihar gaba. Mu a nan Kano, da wahala ka samu tsofaffin gwamnoni sun haɗu domin tattauna hanyoyin da za a magance matsalolin jihar." "Ina kira ga tsofaffin gwamnoninmu, idan har da gaske suna ƙaunar Kano, su haɗa kai. Ba a samun ci gaba da rabuwar kai. Dole jagororin si...
Yarinyar da ake tuhuma da zuba wa miijinta guba a abinci a Jigawa ta amsa laifinta

Yarinyar da ake tuhuma da zuba wa miijinta guba a abinci a Jigawa ta amsa laifinta

Duk Labarai
Yarinyar nan mai shekara 14 da ƴansanda suka tuhuma da kashe abokin mijinta bayan zuba musu guba a abinci a jihar Jigawa ta amsa laifinta a gaban alƙali Al'amarin dai ya faru ne a ranar Lahadin 15 ga watan Disambar 2024 a ƙauyen Bakata da ke ƙaramar hukumar Kiyawan jihar Jigawa. Yarinyar dai ta saka wa mijinta da abokansa guba a taliya, kuma nan da nan suka fita daga hayyacinsu, inda aka kai su asibitin garin Jahun inda a nan ne ɗaya daga cikin abokan mijin ya mutu. Yarinyar ta amsa laifin saka gubar, sai dai kuma ta ce tsohon saurayinta wanda ɗanuwanta ne ya ba ta gubar domin ta saka wa mijin nata da abokansa a abinci. Sai dai tsohon saurayin ya ce ba ya garin lokacin da yarinyar ta je garin. Yanzu haka yarinyar tana tsare a hannun ƴansanda inda shi kuma saurayin ke tsare a gi...