Sunday, January 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Shin maniyyi yana da yauki

Maniyyi
Shin maniyyi yana da yauki? E, maniyyi yana da danko da yauki saboda kayan dake cikinsa kamar su protein da fructose, waɗanda suke taimakawa wajen motsawar kwayoyin halitta. Wannan ya sa maniyyi ke da danko da yauki da kuma saurin motsi. Maniyyin namiji ida ya fito waje za'a ganshi da kauri da kuma yauki. Saidai idan ya dauki lokaci, zai tsinke ya zama kamar ruwa kuma kalarsa zata canja yayi haske ba kamar yanda ya fito da farko ba. Hakanan Maniyyin namiji a daidai lokacin da ya fita, yana da dumi. Kuma yana fitane daya bayan daya. Idan ya gama fita, namiji yakan ji jikinsa ya mutu.

Nasiha akan rayuwa

Magunguna
Rayuwa cike take da gwagwarmaya, wata rana ayi dariya, watarana a yi kuka. Duk yanda za'a juya,ka yi kokari, sannan a yi addu'ar Allah kada ya raba mutum da imaninsa. Kowa na da matsala, ta wani tafi ta wani, kada ka ga mutum cikin manyan kaya da babbar mota ka yi tunanin yana cikin jin dadi, da zai bude maka cikinsa,kai da kake tafiya a kasa watakila ka fishi nutsuwa. Kada ka yawaita bayyana matsalarka a wajan jama'a, ya zamana cewa amininka ne kadai zaka baiwa labarin abinda ke faruwa da kai. Idan ka ji gaba daya duniyar ta canja, ka kasa gane kanka, komai ka gwada yaki yi, ka koma ga Allah,ka yi ta zikiri, ka rika karatun Qur'ani. Ka koma ka nutsu ka duba kanka da yanayin da kake ciki, insha Allahu zaka samu mafita. Ka koyi girmama mutane, saidai kada ka wulakanta kank...

Amfanin hakuri a rayuwa

Magunguna
Hakuri yana da matukar amfani a rayuwa ta hanyoyi da dama: Kiyaye Lafiya: Hakuri na taimakawa wajen rage damuwa da bacin rai, wanda zai iya hana matsalolin lafiya kamar hauhawar jini da ciwon zuciya. Gina Dangantaka Mai Kyau: Hakuri na taimakawa wajen kiyaye dangantaka mai kyau da mutane. Yana taimakawa wajen fahimtar juna da yin sulhu idan an samu sabani. Cimma Manufa: Mutanen da suka kasance da hakuri suna iya cimma burinsu domin ba sa gajiya da sauri, suna ci gaba da aiki har sai sun cimma burinsu. Rage Zafin Rai: Hakuri na taimakawa wajen rage zafin rai da saurin fushi, yana sa mutum ya yi tunani kafin ya dauki mataki mai tsanani. Inganta Kwarewa: A fannin koyo da aiki, hakuri yana sa mutum ya ci gaba da kokari har sai ya samu cikakkiyar kwarewa a abin da yake yi. Ka...

Mallakar miji har abada

Sirrin Mallaka
Mallakar miji har abada yana nufin cikakkiyar soyayya, aminci, da sadaukarwa tsakanin ma'aurata. Wannan ya hada da: Aminci da yarda: Ma'aurata su aminta da juna, su yarda da juna a kowane hali. Wannan yarda tana sa soyayya ta kara shauki. Sadaukarwa: Sadaukarwa tana da matukar muhimmanci wajen mallakar miji har abada. Kowanne daga cikin ma'aurata zai nuna sadaukarwa wajen kula da juna da kuma kyautata wa juna. Hadin kai: Ma'aurata su kasance masu hadin kai a dukkan al'amuran rayuwa, ciki har da shawo kan matsaloli tare. Fahimta: Fahimtar juna yana taimaka wajen kaucewa sabani da kuma samun zaman lafiya a gida. Girmamawa: Girmama juna yana tabbatar da cewa kowanne daga cikin ma'aurata yana ganin kimar dayan. Kula da juna: Kula da juna, musamman a lokacin rashin lafiya...

Addu ar mallakar miji cikin sauki

Sirrin Mallaka
Mallakar miji cikin sauki yana da alaka da kwarewar zaman aure, hakuri, da kuma juriya. Ga wasu shawarwari masu amfani: Girmama Juna: Kula da martabar miji da kuma nuna masa girma yana da muhimmanci. Yi kokarin fahimtar ra’ayinsa da kuma nuna masa cewa kina darajashi. Sadarwa: A kullum, sadarwa mai kyau tana taimakawa wajen warware matsaloli cikin sauki. Ka tabbatar kuna magana game da abubuwan da suka shafe ku duka cikin sauki da gaskiya. Soyayya da Kulawa: Nuna soyayya ta hanyoyi daban-daban, kamar yin kyauta ko aikata abubuwan da suka dace da shi, yana taimakawa wajen bunkasa dangantakarku. Hakuri da Juriya: Kowanne aure yana da kalubale. Kasance mai hakuri da kuma juriya wajen fuskantar kalubalen da ke tunkaro ku. Karfafawa da goyon baya: Ki kasance a shirye don ba ...

Sirrin mallakar miji

Sirrin Mallaka
Mallakar Miji abune da matan aure da yawa ke nema. A wannan rubutu zamu bayyana muku yanda zaki mallaki mijinki sai yanda kika juyashi. Abu na farko da zaki yi ki mallaki mijinki shine kyautatawa. Kyautatawa na da matukar muhimmanci, muna maganar kyautatawa ta fannoni da yawa, wajan bashi abinci, magana,mu'amalar aure da sauransu. Ki Kyautawa mijinki idan ya kawo muku abinci: Kada ki gaji, a duk sanda mijinki ya kawo abinci ki mai godiya, kamar wannan abinci shine na farko da ya taba kawo muku, wannan zai saka mishi kara sonki da kara kaimi wajan ciyar daku,kuma zai kara masa soyayyarki. Ki kyautatawa mijinki a yayin da ya zo fita da lokacin dawowa: Idan mijinki yazo fita ki rika masa addu'a, ki masa addu'ar ya jiki "Mijina Allah ya bada sa'a", "Allah ya dawo mana da kai l...
INDA RANKA: Matar Aure ta ka$he mijinta a Yobe

INDA RANKA: Matar Aure ta ka$he mijinta a Yobe

Auratayya
Wata matar aure ‘yar shekara 22, Zainab Isa ta ka$he mijinta mai shekaru 25, Ibrahim Yahaya a wata rigima da suka yi a gidansu dake Unguwar Abbari da ke Damaturu a jihar Yobe. A Yau ta rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta cafke wacce ake zargin wadda yanzu haka ƴaƴansu Biyu, domin gudanar da binciken musabbabin faruwar lamarin

Sirrin mallaka na gishiri

Sirrin Mallaka
Gishiri na da tasiri sosai abubuwan rayuwar al'umma daban-daban, kama daga abinci, da kuma yanayin rayuwa na yau da kullun. Ana amfani da Gishiri wajan hada sirrin Mallaka, Saidai a yayin da wasu wannan sirri na musu aiki, wasu baya musu aiki. Amma abin tambaya anan shine, menene ingancin sirrin mallaka na gishiri? Masu iya magana sun ce,tsafi gaskiyar maishi, ga wasu, wannan sirri zai yi amfani kamr yanda muka bayyana a sama, ga wasu kuma ba zai yi amfani ba, ya danganta ga karfin imanin mutum akan aikin wannan abu. Babbar Hanyar Mallaka kamar yanda muka bayyana a baya shine ta hanyar kyautatawa a bangaren ma'amala, kyauta,da kuma kalamai masu dadi.

Mallaka da tumfafiya

Mallaka, Sirrin Mallaka
Wa kike so ko kake ka mallaka, Budurwace, Saurayine? Akwai hanyoyin Mallaka da Tumfafiya da ake amfani dasu. Saidai ba kowa ya sansu ba kuma ba kowane yakewa aiki ba sai wanda yayi dace. Amma menene ingancin Amfani da Tumfafiya wajan mallkar wani? Maganar gaskiya itace wannan hanya bata da inganci,zai iya zama sihiri ne ko surkulle wanda zai iya yin aiki, zai kuma iya zama bai yi aiki ba. Ana mallaka ne ta hanyar kyautatawa da mu'amala me kyau. Koma wanene kike so ko kake ka mallaka, babbar hanyar da za'a bi shine kyautatawa. Muna maganar Kyautatawa ta bangaren Kyauta, kalamai, da mu'amala. Misali Idan Mijine: Ki rika kyautata masa ta hanyar tsaftace kanki farko, ya zamana bakinki baya wari, jikinki baya wari, kayan jikinki tsaf-tsaf masu kama jiki da fiddo surar ji...