Mun baku wata daya ku sauko da farashin kayan abinci ko mu daureku>>Gwamnatin Tarayya ga ‘yan kasuwa
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar dake kula da tsaftar gasa a kasuwanci da kiyaye hakkokin masu sayen kaya, FCCPC ta baiwa 'yan kasuwa wata daya su karya farashin kayansu ko su dandana kudarsu.
sabon shugaban hukumar, Mr. Tunji Bello ne ya bayyana haka a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki ranar Alhamis daya gudana a Abuja.
Yace bayar da misalin wani lemu da ake sayarwa a kasar amurka akan $89 wadda yace kwatankwacin Naira 140,000 ne amma a wani babban shagon sayayya dake Legas sun ga ana sayar da lemun akan Naira 944,999.
Yace wannan yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne wanda kuma ba zasu lamunta ba.
Yace duk wanda aka kama akan wannan laifi zai iya fuskantar tara me yawa ko kuma dauri.