Bidiyon batsa na wani Fasto Lucian dan kasar Uganda ya bayyana.
Bidiyon ya bayyana faston yana lalata da matar wadda ba'a san ko wacece ba sannan yana daukar bidiyon da kansa.
Faston dai yayi suna sosai a kasarsa ta Uganda saboda warkewa da yayi daga cutar Ebola.
Saidai tuni ya fito ya karyata cewa bashi bane a cikin bidiyon.
Saidai wadanda suka sanshi sunce lallai shine a Bidiyon.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan hotunan wanda aka dauka daga wajan bikin zagayowar ranar Haihuwarta da ta yi jiya.
Hadiza ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta inda ta cika shekara 35 da haihuwa.
Gwmanatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bai wa ma'aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi - da ta fara biya wata shida ta suka gabata - har zuwa lokacin da za a kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.
Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai ranar Asabar a Abuja, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce wa'adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne ranar, 8 ga watan Afrilun 2024.
Sai dai ministan bai bayyana adadin kuɗin da gwamnatin ke biya a matsayin albashin wucin gadin ba, to a baya gwamnatin ta ce za ta riƙa biyan ma'aikatan ƙarin naira 35,000 a kan albashinsu kowane wata har na tsawon wata shida.
A ranar juma'a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin, kasancewar wa'adin ranar 31...
Wasu Ministocin Isra’ila biyu masu tsatsauran ra’ayi sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin hadin gwiwar ƙasar idan har Benjamin Netanyahu ya amince da tayin sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da shugaba Biden na Amurka ya gabatar.
Yarjejeniyar da Mista Biden ya sanar ta samu karɓuwa daga ɓangaren ƴan adawa a Isra’ila da ƙasashe masu shiga tsakani.
A ranar juma'a ne shugaba Biden ya yi tayin tsagaiwa wutar ta hanyar bullo da matakai uku, da suka haɗa da tsagaita wuta na mako shida a matakin farko.
Tare da janyewar dakarun Isra'ila daga wurare masu yawan jama'a a Gaza.
Sannan ya ce yarjejeniya za ta bayar da damar sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na dindin tare da sake gina Gaza.
To sai dai ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-Gvir, ya ce duk wa...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce jami'anta sun samu nasarar kama muggan ƙwayoyin da kuɗinsu ya kai kimanin naira biliyan 2.1 a biranen Legas da Fatakwal
Cikin sanarwar nasarar mako-mako da hukumar ke fitarwa ta ce a ranar Juma'a 31 ga watan Mayu, jami'anta tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas suka kama wasu manyan jakankuna maƙare ƙulli 320 na tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 164.50 da aka yi safararta daga Canada.
Hukumar ta ce ta kama mutumin da take zargi da safarar tabar - da aka yi ƙiyasin kuɗinta ya kai naira miliyan 960, - mai suna an kama Ughenu Nnaife Francis, wanda ya shaida wa jami'an hukumar cewa naira miliyan shida aka biya shi domin shigar da kayan Najeriya.
NDLEA ta ...
Hukumar Kula da Inganci da Abinci ta Najeriya, NAFDAC ta gargaɗin 'yan ƙasar dangane da amfani da wani sinadarin adana abinci da ake kira Sniper.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa shafinta na intanet ta ce tana ankarar da jama'a game da illar amfani da sinadarin wajen kare abinci daga lalacewa.
Hukumar ta ce tun a shekarar 2019 aka haramta sayarwa da amfani da sinadarin da ke cikin ƙananan ƙwalabe.
Yayin da aka sahalewa sayar da manyan kwabale musamman ga amintattun masu samar da magungunan ƙwari ga manoma.
A baya-bayan nan ne dai wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta a ƙasar ya nuna yadda wasu ke amfani da sinadarin wajen adana nau'o'in abinci, kamar kifi da wake da wasunsu.
Yayin da take mayar da martani kan bidiyon shugabar hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye...
Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ƙarkashin Jagorancin Shéikh Malam Aminu Ibrahim Daurawa Ta Kama Mawaƙin Kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mawakin nan kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh.
Bayanan da Freedom Radio ta samu sun nuna cewa Hisbah ta kama G-Fresh saboda zargin yiwa Alkur’ani Mai Girma Izgili da kuma yin kalaman batsa.
Karin bayani:
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama fitaccen mai amfani da shafukan sada zumuntar nan da aka fi sani da G-Fresh
Babban daraktan hukumar Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar wa BBC labarin kama matashin.
Ya ce hukumar ta kama shi bayan jerin gargaɗin da ta yi masa sakamakon abubuwan da yake wallafawa a shafukan sada zumunta.
''Mun kama shi ne bayan tarin gargadin da muka sha yi masa kan abubuwa...
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata inda take tare da abokin aikinta dan kasar India.
Ta saka hoton a shafinta na sada zumunta:
Kasar Maldives ta zama ta farko data hana mutanen kasar Israela shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa.
Yakin da kasar Israela take yi da Falasdinawa dai ya fara jawo mata Allah wadai har ma daga manyan kasashe.
Kasa ta baya-bayannan data dauki mataki akan kasar Israela itace kasar Faransa wadda ta hana kasar ta Israela halartar taron bajakolin makamai mafi girma a Duniya.