Thursday, January 2
Shadow

Ba A Taɓa Gwamnatin Da Ta Kawo Wa Nijeriya Bàĺà’ì Da Mùśìbà Kamar Gwamnatin Buhari Ba, Cewar Attahiru Bafarawa

Daga Imam Aliyu Indabawa

Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi Allah wadai da masu baiwa Buhari da gwamnatinsa kariya yana mai cewa duk mutumin da zai iya fitowa ya kare Buhari da gwamnatinsa to za su haɗu da shi a lahira a gaban Allah.

A yayin tattaunawarsa da kamfanin watsa labarai na BBC Hausa tsohon gwamnan ya ce,” Bala’in da Buhari ya kawo ƙasar nan na lalacewar damokraɗiya da cin hanci ni dai a rayuwata ban taba ganin gwamnatin da ta kawo mana bala’i da masifa kamar ta Buhari ba.”

Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin Buhari ta ciyowa Nijeriya mummunan bashi na tiriliyoyi amma babu wani aiki da aka yi da kuɗin, ya ce wannan sai an je lahira za a yi shari’a a kansa.

Karanta Wannan  Hotuna: Zai auri mata 2 a rana daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *