Friday, December 5
Shadow

Ba addini ne kawai ke haifar da rikicin Najeriya ba – EU

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba.

Cikin wata sanarwa kakain ƙungiyar da Anouar El Anouni ya fitar ya ce ƙungiyar EU na jajanta wa imjutanen da rikicin ya rutsa da su kudanci da arewa maso gabashin ƙasar.

Matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.

Sai dai EU ta ce akwai abubuwa da dama da ke haifar da rikicin ba addini kaɗai ba.

“Mun fahimci cewa akwai abubuwa masu yawa da ke haifar da rikici a Najeriya, addini guda ne daga cikinsu, amma ba shi kaɗai ba,” in ji Mista El Anouni.

Karanta Wannan  Za'a samu saukin rayuwa, kayan masarufi zasu sauka kasa>>Inji Gwamnatim tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *