
Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, ba dan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba da Najeriya ta rushe.
Ya bayyana hakane a Abuja wajan taron cika shekara 50 na makarantar Horas da sojojin Najeriya dake Zaria
Ribadu ya koka da matsalar tsaro data tattalin Arziki da ake fama da ita a Najeriya, saidai yace Gwamnatin shugaba Tinubu ta yi kokari sosai bisa ayyukan data gudanar.
Yace jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’dda 13,543 a Arewa maso gabas da kuma kashe shuwagabannin ‘yan Bindiga 120 a Arewa maso yamma.
Yace hakanan a Naija Delta ma an an samu ci gaba sosai ta fannin tsaro.