
Gwamnatin tarayya ta yiwa tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso martani kan ikirarin da yayi cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya watsar da yankin Arewa.
Da yakewa Kwankwaso martani, Me magana da yawun shugaban kasar, Daniel Bwala yace Kwankwaso yayi kuskure.
Shugaba Tinubu bai yi twasi da yankin Arewa ba.
Daniel Bwala ya bayyana hakane a shafinsa na X inda ya zayyano irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke yi a Arewa.