
Sojojin Najeriya sun musanta ikirarin dake cewa gawurtaccen me garkuwa da mutane, Bello Turji ya tuba ya mika wuya.
Me magana da yawun sojojin, Maj.-Gen. Markus Kangye ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Alhamis.
Yace Bello Turji bai mika wuya ba har yansu suna bin sahunsa.
Ana zargin Turji da hannu a garkuwa da mutane da kisa da sauransu.