Saturday, August 8
Shadow

Sai mun biya Naira Miliyan 3 ake yadda mu gabatar da kudirin doka a majalisa>>Inji Dan majalisar tarayya Hon. Ibrahim Usman Auyo

Dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa, Hon. Ibrahim Usman Auyo ya yi zargin cewa sai sun biya tsakanin Naira Miliyan 1 zuwa 3 sannan ake yadda su gabatar da kudirin doka a majalisar tarayya har a karantashi a zauren majalisar.

Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa, bayan haka sai mutum ya bi ‘yan majalisar yana rokonsu akan su goyi bayan kudirin nasa.

Yace dan haka maganar gabatar da kudirin doka a majalisar ya zama hanyar samun kudi.

Karanta Wannan  Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Kuje ta dage gurfanar da tsohon Sakataren NHIS, Farfesa Usman Yusuf, zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *