Friday, May 23
Shadow

Ba za mu bari PDP ta nutse da mu ba – Sanatocin Kebbi

Sanatocin Najeriya uku da suka fito daga jihar Kebbi, waɗanda suka sauya sheƙa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki sun ce sun fita daga jam’iyyar ce sanadiyyar rikice-rikice na cikin gida.

A jiya Talata ne shugabancin majalisar dattajai ya tabbatar da sauya shekar sanatocin wato Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta tsakiya da Yahaya Abdullahi mai wakilartar Kebbi arewa da kuma Garba Maidoki mai wakiltar Kebbi ta kudu.

Sanatocin sun ce sun fice daga jam’iyyar ne saboda rikice rikicen cikin gida da suka yi wa jam’iyyar PDP katutu.

Daya daga cikinsu, Sanata Yahaya Abdullahi ya shaida wa BBC cewa a bayyane take tun bayan zaɓen 2023, jam’iyyar PDP ta shiga ruɗani da rikici kala-kala, kuma har kawo yanzu babu alamun jam’iyyar tana ɗaukar matakin gyara matsalolin nata.

Karanta Wannan  Hotuna: 'Yansandan Najeriya sun fara aiki da motar zamani

Ya ce ”Kowa ya san dai abubuwan da suka addabi PDP, tana son ta wargaje. Ba kuwa wanda ke son ya shigo mu’amula da jama’a sai ka ga waɗanda ka zo kana son ka zauna da su kana tsammanin za a haɗa kai a ceto al’umma a gyara ƙasa, sai kansu duk ya rarrabu, abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa kullum sai ƙara lalacewa ya ke.”

Ya yi bayanin cewa ai dama can da su aka kafa APC amma sun fice daga cikin ta ne saboda gwamnan su na wancan lokacin ya nuna baya yi da su, kuma sai PDP ta janye su, amma a yanzu yanayin ya canza domin kuwa asalin ƴan PDP su gaza ɗinke ɓarakar su ta cikin gida kuma ga shi a ”shugaban ƙasa Tinubu ya san amfanin mu, kuma shi sabon gwamna Dr Nasiru Idris Kauran Gwandu ƙaninmu ne, ya bamu girma ya bamu mutumcin mu, don haka irin wannan a kan me za mu zauna muna jayayya da shi.”

Karanta Wannan  Tsohuwar Ministar Jin Kai, Betta Edu da aka sauke saboda zargin karkatar da kudin Talakawa ta samu kyautar girmamawa a jami'ar Calabar

Sanata Yahaya Abdullahi ya kuma musanta cewa akwai alƙawarin da shugaba Tinuu ya yi masu, wanda ya sa suka sauya sheka zuwa APC inda ya ce shi a yanzu babu abin da bai gani ba a rayuwa domin haka ya wuce a yi mashi alƙawari kafin sauya sheƙa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *