Wednesday, November 12
Shadow

Mun shaida tsare-tsaren shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu na aiki yanda ya kamata, sun kawowa Najeriya ci gaba>>Inji Kasar Ingila

Gwamnatin Birtaniya ta ce matakan da shugaban Najeriya bola Ahmed Tinubu ke ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar kwalliya na biyan kuɗin sabulu.

Birtaniyan ta ce matakan da aka ɗauka musamman wajen farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar, da na kuɗin shiga na daga cikin dalilan da suka aka samu ƙaruwar damar zuba jari a ƙasar.

Jakadan Birtaniya a Najeriya Dr. Richard Montgomery ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na aiwatar da shirin bunƙasa tattalin arzikin Najeirya da Birtaniya, ta fuskar kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, da ya gudana a Abuja babban birnin na Najeriya.

Gwamnatin Birtaniyar ta ce la’akari da rahoton da Bankin Duniya a baya-bayan nan kan harkokin zuba jari a Najeriya ya nuna cewar darajar kuɗin ƙasar naira na farfaɗowa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ni Ba Barawo bane shiyasa bana taba kayan Mutane, Kayan Gwamnati kadai nake dauka shima dan nasan ina da hakki a ciki>>Inji Wani Barawo da 'yansanda suka kama

Haka kuma rahoton ya ce ana samun ƙaruwar kuɗaɗe a asusun ƙasashen wajen na ƙasar da kuma na haraji, lamarin da ya sa ake samun buƙatar ƙara faɗaɗa harkokin zuba jari a ƙasar.

Birtaniyan ta ce shirin bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu da suke haɗin gwiwa za a cimma shi ne idan Najeriya ta mayar da hankali kan wajen samar da daidaitacen tsari da zai haɓaka harkokin kasuwanci da janyo hankulan masu zuba jari a ƙasar.

Sai dai ya ce ganin irin matakan da shugaban Najeriya ya ɗauka a ɓangaren tattalin arzikin ƙasar, yasa suka fitar da wasu ɓanagarori takwas da zasu haɗa gwiwa da Najeriya wajen ganin ta haɓaka kasuwacin da yawan masu zuba jari a ƙasar.

Karanta Wannan  Janar Ibrahim Babangida ya amince Abiola ne ya ci zaɓen 1993 da ya rushe

Haka kuma Jakadan Birtaniyar ya ce baiwa kamfanonin ƙasar irin na su Ɗangote suka fara tace man fetur yasa an samu raguwar fitar da ɗanyen man fetur zuwa ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *