Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen jihar Kano, (NMA), ta ce likitocin da ke aiki a asibitocin Kano za su ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ke gudanarwa.
Sakataren ƙungiyar reshen jihar Kano, Dr Abdurrahman Ali, ya shaida wa jaridar Daily Trust ranar Litinin cewa ” mu ƙwararru ne saboda haka ba a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago muke kuma saboda haka ba za mu shiga yajin aiki ba”.
Ya ƙara da cewa “dukkannin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya za su ci gaba da kasancewa a wuraren aikinsu. Bai zama lallai a cimma hakan ɗari bisa ɗari ba amma dai ba za mu shiga yajin aikn ba. E akwai yiwuwar ka je ka ga ma’aikacin da zai fito da fayil ɗinka ba ya nan amma kuma mambobinmu za su kasance a wuraren aikinsu.”