Friday, June 26
Shadow

Fârgaba Yayin Da Sarki Sanusi, Aminu Ado Bayero Suka Sanar Da Jagòrantar Sâllar Juma’a A Masallaci Ɗaya, Shin me zai faru?

DAGA: Abbas Yakubu Yaura

Tsòro ya mamaye tsòhon birnin Kano yayin da sarakunan biyu da ke hamayya da juna – Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka dawò dashi da Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da aka tsige suka bayyana shirinsu na yin sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na fadar Sarkin.

Majiyar mu ta rawaito cêwa tuni mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ke zaune a fadar, kuma kusa da Masallacin da ake fafatawa, ana sa ran zai jagoranci sallar Juma’a raka’a biyu.

Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagòranci Sallar Juma’a a babban masallacin fadar a matsayin sarkin birnin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Karanta Wannan  An bada shawarar cewa, Tunda dai abu yaki ci yaki cinyewa tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero to kawai a hada Musabaka, wanda yaci sai a bashi sarautar

Sanarwar mai dauke da sa hannun Danburan Kanò, Munir Sanusi Bayero, ta bayyana matsayar Maimartaba Sarkin Kanò Muhammadu Sanusi II zuwa Masallacin dómin jagorantar Sallar Juma’a.

An fitar da sanarwar a daren Ranar Alhamis.

Sanarwar ta Danburan ta gayyaci mazauna Kano da su zo su saurari wa’azin da Sarki Malam Muhammadu Sanusi II zai gabatar.

Sai dai kuma wata sanarwa daga wani hadimin mai martaba Sarkin, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gayyaci jama’ar yankin da su zo tare da shi a masallacin Juma’ar na fadar Sarkin domin gudanar da sallar Juma’a.

An bayyana cewa za a fara tafiya zuwa Masallacin fadar Sarkin da karfe 12:30 na rana.

Karanta Wannan  Kamin ka samu mutum 1 da baya son mahaifina sai ka samu 10 masu sonsa>>Inji Dan Sarki Muhammad Sanusi II, Ashraf Sanusi

Sai dai har yanzu ‘yan sandan ba su ce uffan ba kan wannan ci gaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *