
Ministan wutar lantarki, Mr Adebayo Adelabu ya bayar da tabbacin samar da tsayayyar wutar Lantarki a shekarar 2026.
Me baiwa ministan Shawara game da sadarwa da hulda da jama’a, Mr Bolaji Tunji. Ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a wata sanarwa da ya fitar.
Yace hakan na kunshene a cikin sakon sabuwar Shekara inda yace Gwamnati zata mayar da hankali wajan samar da tsayayyar wutar lantarki ga gidaje da masana’antu.