
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, ba za’a iya samun zaben gaskiya ba a Najeriya.
Goodluck Jonathan ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar inda yace babbar matsalar itace akwai masu zabe da ake amfani dasu wadanda babu su a zahiri.
Jonathan yace sai an samu shuwagabannin hukumar zabe masu nagarta wadanda da su yi magudi kara su sauka daga mukaminsu kamin a samu abinda ake so.
Yace ba hujja bace shugaban hukumar zabe yace wai matsa masa aka yi yayi magudi ba, idan aka matsama sai kace gara ka sauka daka aikata ba daidai ba.