Friday, December 6
Shadow

Kungiyar Masu Hako danyen Man fetur a Najeriya sun gargadi Gwamnati akan baiwa ‘yan kasuwa lasisin shigo da man fetur Najeriya

Kungiyar kamfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya, CORAN ta gargadi Gwamnatin tarayya ta yi hankali da baiwa ‘yan kasuwa lasisin shigo da man fetur daga kasashen waje.

Hakan na zuwane a yayin da baraka ta faru tsakanin ‘yan kasuwar da Matatar man fetur ta Dangote inda aka shiga kotu, ‘yan kasuwar na neman a basu lasisin shigo da man fetur din daga kasar waje saboda sun ce man fetur din Dangote yayi tsada amma shi kuma yana neman kada a basu lasisin saboda a cewarsa zasu shigo da man fetur din da bai da inganci wanda gurbataccene.

A sanarwar da kungiyar CORAN ta fitar ta bakin Sakataren yada labaranta, Eche Idoko tace abin damuwa ne yanda ‘yan kasuwar suka nace sai sun shigo da man fetur din daga kasar waje.

Karanta Wannan  Ko Kun Kula Cewa Hussaina Matar Soja Abbas Bai Karbu Sosai A Wajen Matan Sòšhìýal Mìďìýa Ba, Duk Da Cewa Labarinta Yana Da Sosa Zuciya?

Yace ‘yan kasuwar suna son mayar da Najeriya wajan kawo man fetur gurbatacce wanda turawa suka ce basu so saboda shine ke da arha.

Yace suna baiwa hukumar NMDPRA wadda itace ke bayar da lasisin shigo da man fetur din shawarar ta daina bayar da lasisin, yace kamata yayi ace sai idan an samu karancin man fetur dinne za’a bayar da lasisin amma ba wai dan a rika gasa da matatun man fetur na cikin gida ba.

Yace Ba suna gayawa NMDPRA yanda zasu yi aikinsu bane suna bayar da shawara ne kan a baiwa ‘yan kasuwar cikin gida da matatun man fetur na cikin gida kariya.

Karanta Wannan  Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *