Friday, December 5
Shadow

Ba zami iya biyan sama da Naira Dubu sittin(60,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta jaddadawa Kungiyar Kwadago cewa, ba zata iya biyan Sama da Naira Dubu 60 ba a matsayin mafi karancin Albashi ba.

Hakan na zuwane a Yau, Litinin da kungiyar ta kwadago ta fara yajin aikin sai baba ta gani.

Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya bayyanawa kungiyar kwadagon da ma’aikatan gwamnatin tarayya cewa tafiya zuwa yajin aiki sabawa doka ne.

Yace kuma zasu iya fuskantar daurin watanni 6 saboda tafiya yajin aikin.

Ya bayyana cewa, har yanzu akwai tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar kwadagon kuma ba’a kammala ba dan haka bai kamata kungiyar ta tafi yajin aiki ba.

Karanta Wannan  Kan mu ya daure, Bamu san wanne hukunci zamu yi amfani dashi ba>>Hukumar 'yansandan jihar Kano bayan da aka aika mata hukunce-hukuncen kotu har 5 da suka shafi masarautar Kano, saidai ta bayyana abinda zata yi nan gaba

Ya roki kungiyar kwadagon data sake tunani kan wannan mataki data dauka inda yace bai kamata ba dan zai jefa da yawan ‘yan Najeriya cikin halin kaka nikayi da wahala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *