Friday, December 5
Shadow

Ba zamu zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba saboda giya zai ta kawowa Arewa>>Inji wani Jigo a APC

Saboda Zai Sa A Shigo Da Giya Arewa, Don Haka Ba Za Mu Zabi Peter Obi Ba — Jigo a Jam’iyyar APC

Wani jigo daga yankin Arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alwan Hassan, ya bayyana cewa Arewa ba za ta kada kuri’a ga Peter Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba, saboda yadda ake alakanta shi da kasuwancin shigo da giya.

Yayin da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata, Hassan ya caccaki Obi bisa yadda ya yaba da kamfanin giya a jihar Anambra da kuma rawar da yake takawa a harkar shigo da barasa.

“Wa kuke tsammani zai kayar da Asiwaju a 2027? Obi wanda a shirin nan yana rokon goyon bayan Arewa, amma a lokaci guda yana murnar girman kamfanin giya a jiharsa kuma yana da hannu a shigo da barasa mafi yawa,” in ji shi.

Karanta Wannan  Kasar Burkina Faso ya dakatar da shigar mata da kayan Gwanjo daga kasar Amurka

“Yanzu kuke so Arewa ta kada masa kuri’a? Za mu kada kuri’a ga wanda zai shigo mana da giya a Arewa?”

Hassan ya jaddada cewa Obi bai dace da ra’ayoyin al’ummar Arewa ba, musamman ganin yadda addinin Musulunci ke haramta giya.

Tun bayan da Obi ya sanar da kudurinsa na takara da alkawarin yin wa’adin shekara daya kacal, yana ci gaba da fuskantar suka daga jiga-jigan jam’iyyar APC.

Har ila yau, Hassan ya ce haɗakar jam’iyyun adawa karkashin tutar African Democratic Congress (ADC) ba wani abu ba ne illa hadin kai na mutanen da ke da kwadayin mulki.

“ADC hadin kan masu fushi ne kawai da tsarin mulki. Kowa daga cikinsu yana son zama shugaban kasa. Amma Asiwaju zai ci gaba da mulki,” in ji shi.

Karanta Wannan  Ka shiga taitayinka, naga take-takenka baka a da'a>>Shugaba Tinubu ya gargadi Sanata Ali Ndume bayan da yace 'yan Najeriya na cikin wahala

Obi, tare da sauran fitattun ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, da Nasir El-Rufai, suna cikin masu adawa da gwamnatin Tinubu da suka kafa hadakar adawa don kalubalantar APC a 2027.

Amma a cewar Hassan, wannan hadakar ba za ta kai ga nasara ba. “Da yardar Allah, Tinubu zai sake lashe zabe a 2027,” ya jaddada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *