Wednesday, November 12
Shadow

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja da Legas kadai

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur dinsa a Abuja da Legas zuwa Naira 875 da kuma Naira 900.

Hakan na zuwane kwanaki bayan da NNPCL din ya kara farashin zuwa Naira N915 da kuma Naira N955.

Saidai a ranar Laraba, kafar TheCable ta ruwaito cewa, ta lura kamfanin ya rage farashin zuwa Naira 40 akan kowacce lita.

A legas, Farashin ya ragu zuwa N875, sannan a Abuja farashin aguwa yayi zuwa N900.

Saidai rahoton yace Dangote da Mobil da AP duka basu rage farashinsu ba yana nan a Naira 915 kan kowace lita.

Karanta Wannan  Ni 'yan uwana ba 'yan gargajiya bane kuma ni gyaran tarbiyya nake>>Martanin GFresh Al-amin ga wanda kw cewa shima 'yan uwansa su zaneshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *