Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya musanta rahotannin dake yawo cewa, wai an kwace masa fili a babban birnin tarayya, Abuja.
Buhari ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu Inda yace shugaba Buharin Nada fili a Abuja amma ba’a kwaceshi ba.
Yace filin da ake magana akai na wata gidauniya ce da aka sawa sunan tsohon shugaban kasar kuma ba mallakin tsohon shugaban kasar bace.
Yace hukumar kula da filaye ta Abuja da gangan ta tsawwala kudi ga masu gidauniyar a yayin da suka je Neman shaidar mallakar filin watau CofO.
Yace koda a lokacin da Buhari ke shugaban kasa an kawo fom wanda zai cike a bashi fili a Abuja amma yace baya so Dan yana da filin.