
Rundunar ‘yansandan Najeriya a Abuja babban birnin Najeriya ta ce jami’inta da aka bayar da rahotonnin cewa an sace ya koma gida tuni.
Da take tabbatar wa da BBC ta wayar tarho, kakakin rundunar Josephine Addeh ta ce da ma ba wani mummunan abu ne ya faru da Sufuritanda Modestus Ojiebe ba.
“Motarsa ce ta samu matsala kawai a kan hanya, kuma gaba ɗaya abin da ya faru bai fi ‘yan awanni ba ya kuɓuta kuma ya koma gida,” in ji ta.
Tun da farko was kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa motar ɗansandan ce ta samu matsala a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna, inda wasu da ake zargin masu garkuwa ne suka yi awon gaba da shi.