Monday, December 16
Shadow

Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ya ziyarci jihar Sokoto game da Làkùràwà

Mai riƙon muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftana Janar Olufemi Oluyede ya nemi da a haɗakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin arewa maso yamma.

Janar Oluyede ya yi kiran ne a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a jihar Sokoto a jiya Lahadi, inda ya ziyarci sansanin dakarun da ke Tangaza da Illela.

A kwanakin nan ne aka samu ɓullar wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ta addabi yankin jihar Sokoto da Kebbi, wadda ake wa laƙabi da Lakurawa, da aka ce ta fito ne daga yankin Sahel.

A ranar Juma’a al’ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar Kebbi suka rasa mutum aƙalla 15 a wani artabu da suka yi da mayaƙan ƙungiyar ta Lakurawa.

Karanta Wannan  Kalli Wani tsohon Bidiyo na Nazir Ahmad Sarkin Waka da ya dauki hankula

Yayin da ya ziyarci sansanonin Janar Oluyed, ya yaba wa sojojin tare da ba su tabbacin samun cikakken goyon baya a aikinsu na yaƙar ‘yan ta’adda tare da magance ƙalubalan da ke fuskantarsu a aiki, bayan da aka yi masa bayani kan halin tsaron da ake ciki a yankin.

Babban hafsan sojin na ƙasa ya nemi a samar da haɗin kai tsakanin al’ummomin yankin da jami’an tsaro a lokacin da yake ganawa da shugaban ƙaramar hukumar Tangaza, inda ya yi kira ga jama’a da su riƙa bai wa dakarun goyon baya da kuma bayanai masu amfani, inda ya ce da taimakon jama’a ne za a iya tabbatar da tsaro a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.

Karanta Wannan  Najeriya ta zo ta 5 a Duniya wajan yawan masu amfani da kafafen sada zumunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *