Babban lauya,Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da gwamnatin Tinubu ta gabatar a gaban kotun tarayya dake Abuja a kotu bisa zargin cin amanar kasa.
Femi Falana wanda lauyane na kare hakkin bil’adama ya bayyana cewa kotun bata da hurumin tuhumar yaran.
Yace kotun ta gaggauta sakinsu sannan kuma gwamnati ta dauki nauyin karatunsu akalla zuwa sakandare ko jami’a.
Yace ko da sun aikata laifi, ba tare da manyan mutane za’a yanke musu hukunci ba dolene a kaisu inda ake yankewa yara hukunci.