Friday, December 6
Shadow

Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari’a

Babban lauya,Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da gwamnatin Tinubu ta gabatar a gaban kotun tarayya dake Abuja a kotu bisa zargin cin amanar kasa.

Femi Falana wanda lauyane na kare hakkin bil’adama ya bayyana cewa kotun bata da hurumin tuhumar yaran.

Yace kotun ta gaggauta sakinsu sannan kuma gwamnati ta dauki nauyin karatunsu akalla zuwa sakandare ko jami’a.

Yace ko da sun aikata laifi, ba tare da manyan mutane za’a yanke musu hukunci ba dolene a kaisu inda ake yankewa yara hukunci.

Karanta Wannan  Za'a rataye matar da ta hallaka tsohon mijinta a Kebbi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *