
Daya daga cikin manyan yaran tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru me suna Hon. Zakari Kafin Hausa ya fice daga jam’iyyar APC.
A sakon da ya fitar dake ta yawo a kafafen sada zumunta yace ya fice daga jam’iyyar APC saboda tana saka mutane cikin damuwa.
Sannan yayi kira ga duka mabiyansa suma su fice daga jam’iyyar.