Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu kananan yara a cikin wadanda ta gabatar a kotu da take zargi da cin amanar kasa ta hanyar kifar da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad.
Lauyan Gwanatin, Rimazonte Ezekiel ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.
Ya kara da cewa, laifin su shine suna kiran sojoji su kwace mulki da daga tutar kasashen waje da kuma tayar da hankula.
Saidai da yawa sun kalubalanceshi da cewa maganar tasa ba gaskiya bane musamman tunda gashi mutane na gani yara ne suka gabatar.
A baya dai hutudole ya kawo muku yanda kakakin ‘yansandan Najeriya ya kare kama yaran inda yace doka tace ko da shekaru 7 za’a iya kaishi kotu.
Ya kara da cewa kuma cikin yaran da aka kama me mafi karancin shekaru shine me shekaru 13.