A yayin da ‘yan kasa ke fama da abincin da zasu ci da kyar, Gwamnatin tarayya ta bayar da gyaran titunan da jirgin saman shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ke bi akan Naira Biliyan 9.8.
Hakanan za’a gyara Titunan zuwa dakin dafa abinci na shugaban kasar da titunan da ake bi dan kai masa ziyara.
Sakataren hukumar ci gaban babban birnin tarayya Abuja, Shehu Ahmad ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace an baiwa kamfanin Julius Berger Plc aikin kuma an basu nan da watanni 6 su kammalashi.
Yace idan aka lura za’a ga cewa titunan tabbas suna bukatar gyara.
Saida kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi Allah wadai da wannan aiki inda sukace kamata yayi a bayar da wadannan kudade wajan inganta rayuwar talakawa.