Monday, December 9
Shadow

Babu kananan yara a cikin wadanda muka kai kotu, duk manyan mutanene wasunsu ma suna da aure>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu kananan yara a cikin wadanda ta gabatar a kotu da take zargi da cin amanar kasa ta hanyar kifar da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad.

Lauyan Gwanatin, Rimazonte Ezekiel ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.

Ya kara da cewa, laifin su shine suna kiran sojoji su kwace mulki da daga tutar kasashen waje da kuma tayar da hankula.

Saidai da yawa sun kalubalanceshi da cewa maganar tasa ba gaskiya bane musamman tunda gashi mutane na gani yara ne suka gabatar.

Karanta Wannan  BABBAR MAGANA: Gwamnatin Kano Ta Maka Mawaki Rarara A Kotu Bayan Sake Wata Waƙar Da Ya Yi Ba Tare Da Hukumar Tace Finafinai Ta Tace Ba

A baya dai hutudole ya kawo muku yanda kakakin ‘yansandan Najeriya ya kare kama yaran inda yace doka tace ko da shekaru 7 za’a iya kaishi kotu.

Ya kara da cewa kuma cikin yaran da aka kama me mafi karancin shekaru shine me shekaru 13.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *