
Basaraken jihar Bayelsa kuma shugaban sarakunan jihar, Bubaraye Dakolo Agada IV, ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya sauke Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio.
Ya bayyana cewa saboda wannan dan zargin da sanata Natasha Akpoti ta yi masa, bai isa ya sa a saukeshi ba.
Yace su suna tare da Sanata Godswill Akpabio saboda dansu ne.
Yace ya kamata awa Sanata Akpabio adalci kuma a kafa kwamitin bincikw da zai binciki lamarin.
Yace Sanata Godswill Akpabio ya kawowa Najeriya ci gaba sosai.