
Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta ikirarin tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar cewa akwai yunwa a Najeriya.
Atiku yace yunwar dake Najeriya da Talauci ka iya tunzura mutane su fita zanga-zanga irin wadda ake yi a kasashen Duniya.
Saidai me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya musanta maganar ta Atiku inda yace Atiku be san halin da Najeriya take ciki ba a yanzu dan an kama hanyar ci gaba.
Yace Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta fitar da bayanai cewa farashin kayan masarufi sun yi kasa, sannan a baya tace kudaden shigar Najeriya sun karu ta bangaren da ba na man fetur ba.
Sannan yace Tinubu ya biya basuka da yawa da ake bin Najeriya.
Yace kuma Tinubu ya dauki matakai na gyara kasa ba tare da tsoro ba.