
Wannan Bafulatanin ya dauki hankula bayan da ya bayyana irin cin zalin da ‘yan Bijilante suka masa.
Ya bayyana cewa ya siyo sabon mashin, shine ‘yan Bijilante suka tareshi akan hanyar komawa gida suka ce sai ya basu dubu 10.
Shi kuma yaki amincewa shine suka masa dukan kawo wuka suka kwace masa kudi dubu 40 da Power bank.
Yace sai da aka kwantar dashi a asibiti.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tiktok.