Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, bai kamata shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dorawa Buhari ko wane irin laifi ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Sunnewsonline.
Yace dalilin da yasa yace haka shine Tinubu yayi Alkawrin dorawa akan inda shugaba Buhari ya gama mulkinsa.
Da aka tambayeshi ko me zai ce kan matsin rayuwar da ake ciki, Buba Galadima ya kada baki yace ai ‘yan Najeriya ne suka siyowa kansu da kudinsu.
Yace sai da ya gargadi mutane amma suka kiya.