Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour Party a shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa babu wata yarjejeniyar hadaka da aka cimma tsakaninsa da wata jam’iyyar Adawa.
Peter Obi ya bayyana hakanne a Abuja yayin ganawa da manema labarai.
Saidai bai karyata cewa akwai tattaunawa da ake tsakaninsa da jam’iyyun Adawa ba amma yace ba’a cimma yarjejeniya ba.
Peter Obi ya bayyana cewa akwai bukatar samun hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da banbancin Jam’iyya ba inda yace ta hakane kadai za’a samu nasarar kwace mulki daga hannun APC dake mulkin kama karya a Najeriya.
Ya bayyana damuwa kan cewa ‘yan Najeriya da yawa bmna bakuntar Lahira basu shirya ba saboda matsalolin tsaro da gwamnati ta kasa shawo kansu