
Daya daga cikin mawakan Kwankwasiyya, Tijjani Gandu ya fito ya bayyana cewa basa son Rabuwar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya bayyana cewa ba wai basa son Abba ya bar NNPP bane.
Amma abinda suke cewa, shine Duk inda Abba zai tafi, su tafi tare da Kwankwaso.
Hakan na zuwane bayan da rade-radi suka yi yawa cewa, Abba zai koma jam’iyyar APC.
Rade-radin sun kara karfi bayan da aka ga Abba ya gana da shuwagabannin jam’iyyar APC na Kano.